Jaridar Daily Trusta ta Nigeria ta nakalto wata majiyar fadar shugaban kasa tana cewa gwamnatin shugaban Buhari ba zata saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ba saboda matsalolin tsaron kasa da kuma kare bukatun mutanen kasa.
Daily Trust ta kara da cewa wani babban jami'am gwamnatin kasar wanda bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana mata cewa matsalar tsare Sheikh El-zakzagy ba ta sharia kadai ba, sai dai ta shafi harkokin tsaron kasar da kuma bukatun mutanen kasar.
Jami'an ya kara da cewa babban abinda sashe na 14(2) na kundin tsarin mulkin kasar ta tanadar a bangaren tsarin tafiyar da gwamnatin shi biyan bukatun al-ummar kasa da bukatar wani mutum guda ba.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin tarayyar tana nazarin labarin ta yadda zata sanya bukatun kasa da tsaronta su zama a sama da kome.
Dangane da masar Sheik Ibrahim El-zakzagy kuma majiyar ta bayyana cewa tana tare da mijinta don kula da shi, idan kuma ta zabi tafiya a cikin yan sa'oee ana iya shirya tafiyarta,288